Gumi ya shawarci Atiku ya garzaya kotu don kwatar mulki daga hannun Buhari

Gumi ya shawarci Atiku ya garzaya kotu don kwatar mulki daga hannun Buhari

Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan dake zaune a jahar Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya shawarci tsohon dan takarar shugabancin kasar Najeriya na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya tabbata ya garzaya kotu domin kwatar hakkinsa.

Gumi ya bayyana haka ne cikin wata budaddiyar wasika daya rubuta a shafinsa na Facebook, inda yayi kira ga Atiku da kasa ya kuskura ya amince da sakamakon zaben da hukumar INEC ta sanar, sakamakon daya bayyanasu a matsayin bogi.

KU KARANTA: Cikakken jawabin da Buhari ya yi bayan INEC ta sanar da nasarar daya samu

Gumi ya shawarci Atiku ya garzaya kotu don kwatar mulki daga hannun Buhari
Malam Gumi
Asali: Twitter

Legit.ng ta ruwaito a daren Laraba ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, inda ya samu kuri’u miliyan 15.19, yayin da Atiku Abubakar ya samu miliyan 11.26.

Don haka yake kira ga Atiku da ba tare da wani bata lokaci bay a garzaya kotu domin ya karbe mulki daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari domin a cewarsa Buhari yayi amfani da karfin iko ne wajen yin magudin zabe.

“Ina jinjina ma Atiku Abubakar saboda jajircewar daya nuna tare da kalubalantar gwamnatin da ake shugabancin kama karya, tabbas ya ceci kasarnan ta hanyar da tarihi ba zai manta dashi ba, don haka ina kira gareshi daya yi watsi da sakamakon bogin da aka sanar.

“Kada ya sake ya bayyana zaben da aka yi a matsayin na gaskiya da gaskiya, kuma ya garzaya kotu domin kwatar hakkinsa, kamar yadda shugaban kasa yayi a baya, shi yafi kowa sanin idan an zalunceshi.

“Wani abu guda da nake da yakini akai shine akwai bukatar sauya fasalin kasarnan, hukumar INEC na bukatar a canzata gaba daya ta yadda za’a dinga zaben shugaban hukumar, kamar yadda ake yi a wasu kasashe.” Inji shi.

Daga karshe Gumi yayi kira ga gwamnati da ta tabbata ta saki duk wasu mutanen data kama da sunan siyasa, kuma Allah ya kareshi daga sharrin abinda yake gani da ma wanda baya gani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel