Bidiyon Buhari da Amosun yayin da ake fadin sakamakon zabe a fadar Aso Villa

Bidiyon Buhari da Amosun yayin da ake fadin sakamakon zabe a fadar Aso Villa

- An ga bidiyon Shugaba Buhari yana kallon sakamakon zaben da aka yi

- Shugaban kasar yana tare ne da Gwamnan Jihar Ogun a fadar Aso Villa

Mun ji labari cewa an dauki shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Ogun Sanata Ibikunle Amosun, su na tare a lokacin da ake shirin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi yau dinnan.

Alakar shugaba Muhammadu Buhari da kuma Ibikunle Amosun tayi nisa domin kuwa sun shaku tun ba yau ba. Ma’aikatan fadar shugaban kasar sun dauki bidiyon Buhari da Aminin na sa su na a bayyana wanda ya ci zabe.

KU KARANTA: APC ta nemi ayi watsi da zaben da aka yi a wata Jihar Kudu

Kwanakin baya an samu matsala a jihar Ogun lokacin da shugaba Buhari ya je yawon yakin neman zabe. An samu ‘yan hamayya na jam’iyyar APM da ke tare da shi gwamna Amosun da su ka rika jifar tawagar shugaban kasa.

A karshe dai hukumar INEC ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da aka yi inda ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa PDP. Shugaba Buhari ya ba Atiku ratar sama da miliyan 3 a zaben da aka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel