Na gode da ku ka sake mara mani baya a wani karon – Buhari ga ‘Yan Najeriya

Na gode da ku ka sake mara mani baya a wani karon – Buhari ga ‘Yan Najeriya

Mun samu labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari har ya furta jawabin a dalilin nasarar da ya sa samu a zaben da aka yi kwanan nan a Najeriya na takarar shugaban kasa da kuma ‘yan majalisu.

Na gode da ku ka sake mara mani baya a wani karon – Buhari ga ‘Yan Najeriya
Ta tabbata cewa Buhari zai cigaba da mulkin Najeriya
Asali: UGC

A yau ne cikin dare, hukumar nan ta INEC mai zaman kan-ta, ta tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da aka yi. Shugaban kasar ya bayyana cewa yayi farin cikin sake zaben sa da jama’a su ka yi.

Shugaba Buhari yake cewa kan sa a kasa, yana mai murnar ganin yadda mutanen Najeriya fiye da miliyan 15 su ka ga cewa ya dace ya sake cigaba da jan ragamar kasar nan na wasu shekaru hudu masu zuwa har shekarar 2023.

KU KARANTA: 2019: An fadawa Atiku ya kira Shugaba Buhari a waya

Buhari yayi wannan jawabi ne a lokacin da yake magana a sakatariyar yakin neman sa na APC da ke babban birnin tarayya Abuja. Shugaban kasar ya kuma godewa mutanen sa da duk wadanda su kayi kokarin ganin ya zarce.

Bayan an yi kwanaki kusan 3 ana kirga kuri’un zaben na bana, an bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri’a 15,191,847 yayin da Atiku Abubakar na PDP ya samu kuri’a 11,262,978.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel