Sai karfe 3 INEC za ta sanar da wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019

Sai karfe 3 INEC za ta sanar da wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019

A halin yanzu dai kididigar kuri'un zabe na jihohin 36 na Najeriya har da babban birnin tarayya Abuja sun nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ne ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2019 da kuri'u 15,191,847.

Sai dai kawo yanzu baturen zabe na zaben shugaban kasa kuma shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu bai riga ya sanar da dan takarar da ya lashe zaben ba.

Bayan amsa tambayoyi da sauraron sharhi da korafi daga wakilan jam'iyoyi da masu sanya idanu a kan zabe da 'yan jarida da sauran al'umma, Farfesa Yakubu ya ce za a dan huta na wasu sa'o'i har zuwa karfe 3 na dare kafin a sanar da wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2019.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani

Zabe 2019: INEC za ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa karfe 3 na yau

Zabe 2019: INEC za ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa karfe 3 na yau
Source: Twitter

A halin yanzu dai magoya bayan jam'iyyar APC tuni sun fara murna samun nasara duba da cewa kuri'un da Shugaba Muhammadu Buhari na APC ya samu ya dara na dan takarar PDP, Atiku Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel