Zaben 2019: EFCC ta kama kwamishinan kudi da babban akawu na jihar Kwara

Zaben 2019: EFCC ta kama kwamishinan kudi da babban akawu na jihar Kwara

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Arzikin Kasa Zagon Kasa EFCC ta tsare kwamishinan kudi da babban akawu na jihar Kwara saboda zarginsu da karkatar da kudin domin amfani da shi a zaben 2019.

Wata majiyar EFCC ta shaidawa Daily Trust cewa an damke mutane biyu a ofishin hukumar na jihar Kwara domin suyi bayani a kan kudi Naira Biliyan daya da suka karba daga wani bankin 'yan kasuwa a jihar kwanaki kadan kafin zabe.

An gano cewar an rike kwamishinan kudi na jihar, Nurudeen Banu da Akanta Janar na jihar, Sulaiman Ishola domin suyi bayani a kan dalilin da yasa suka karbi kudin da abinda suka aikata da shi.

DUBA WANNAN: Cin zaben APC: Dubban al'umma sun mamaye titunan Sokoto

EFCC ta damke kwamishinan kudi da babban akawu na jihar Kwara
EFCC ta damke kwamishinan kudi da babban akawu na jihar Kwara
Asali: Facebook

Kungiyar KWARA-CGGA ta bukaci EFCC ta binciki gwamnatin jihar na Kwara a kan bashin na Naira Biliyan Daya da ta karba daga bakin kwanaki kadan gabanin babban zaben.

Sakatare Janar na Kungiyar, Hassan Omoiya ya ce bayannan sirrin da suka samu ya nuna cewa gwamnatin jihar ta karbi bashin a ranar 13 ga watan Fabrairu a hannun wani banki inda su kayi amfani da harajin jihar Kwara a matsayin jingina a watan Fabrairun da Maris din 2019.

Ya ce, "Muna kira ga Hukumar EFCC da Ma'aikatan Kudi su suyi bincike a kan bashin Naira Biliyan Daya Gwamnatin Jihar Kwara ta karba daf da babban zabe."

"Kuma yin amfani da asusun haraji na jiha a matsayin jingina wurin karbar bashin ba tare da amincewar hukumar karban bashi da ma'aikatan kudi ba ya sabawa dokokin bayar da bashi a gwamnatin jihar.

"Muna sa ran binciken da za ku gudanar zai kai ga mutane da kamfanonin da suke da hannu cikin bayar da wannan bashin tare da sa ran za a hukunta duk wadanda aka samu da laifi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel