Yanzu-yanzu: Hukumar Soji ta damke kwamishana, dan majalisa dokoki, soja 1, yan sanda 3 da takardun kuri'a

Yanzu-yanzu: Hukumar Soji ta damke kwamishana, dan majalisa dokoki, soja 1, yan sanda 3 da takardun kuri'a

Akalla mutane 13 sun shiga hannun hukumar sojin Najeriya kan laifin mallakan takardun kuri'u da karban cin hanci a ranan zaben shugaban kasa da yan majalisu da ya gudana ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

Daga cikin wadanda aka kama sune kwamishanan raya biranen jihar Ribas, Reason Williams da dan majalisan dokokin jihar Ribas, Opokri Wanaka.

Sauran sune jami'an soja, yan sanda uku da ake tuhuma da karban kudade domin kawo hargitsi kan kayayyakin zabe da aka ajiye a babban bankin CBN dake jihar Rivers.

Aminu Iliyasu, kakakin hukumar sojin 6 Division na garin Fatakwal ya bayyana hakan ne yayinda aka bayyanasu a ranan Talata, 26 ga watan Febrairu, 2019.

Yanzu-yanzu: Hukumar Soji ta damke kwamishana, dan majalisa dokoki, soja 1, yan sanda 3 da takardun kuri'a
Yanzu-yanzu: Hukumar Soji ta damke kwamishana, dan majalisa dokoki, soja 1, yan sanda 3 da takardun kuri'a
Asali: Facebook

KU KARANTA: El-Rufa'i ya gana da Buhari a kan kisan mutane a Kajuru

Mun kawo muku rahoton cewa Hukumar sojin Najeriya ta damke akalla mutane takwas dake da hannu wajen tayar da tarzoma a zaben da aka gudanar ranan Asabar a jihar Ribas.

Yayinda hukumar ke bayyana yan barandan a garin Fatakwal ranan Talata, kakakin hukumar, Sagir Musa, ya ce yan barandan sun bayyana cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, suke yiwa aiki.

Yace yan barandan sun sanya kaya kaman ma'aikatan hukumar INEC kuma suka kawo matsala wajen zabe.

Kana ya tabbatar da cewa sun samu faifan odiyon maganar yan barandan da gwamnan.

An bayyanasu a hedkwatan hukumar Soji dake jihar kuma an kai inda suka ajiye motar gidan gwamnatin jihar wacce sukayi amfani da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel