Yanzu Yanzu: PDP ta bukaci INEC ta dakatar da sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa

Yanzu Yanzu: PDP ta bukaci INEC ta dakatar da sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira ga Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Mahmood Yakubu da ya dakatar da sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa.

Jam’iyyar tayi wannan kira ne a wani taron manema labarai tab akin mataimakin daraktan kamfen din Shugaban kasa na PDP, Kabiru Turaki, tare da sauran jami’an jam’iyyar a daren ranar Talata, 26 ga watan Fabrairu a Abuja.

Jam’iyyar tace INEC ta dakatar da sanarwar har sai INEC ta saki adadin wadanda na’urar tantance masu zabe ta tantance a zabe.

Yanzu Yanzu: PDP ta bukaci INEC ta dakatar da sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa
Yanzu Yanzu: PDP ta bukaci INEC ta dakatar da sanar da sakamakon zaben Shugaban kasa
Asali: Original

Tayi zargin cewa an soke kuri’un da aka kada a wuraren da take da karfi musamman a "Yobe, Nasarawa, Zamfara da Plateau.”

KU KARANTA KUMA: PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Shugaban kasa da na majalisa a Kano

A baya mun ji cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta ki amincewa da sakamakon zaben Shugaban kasa daga jihar Katsina kan zargin rashin bin ka’ida.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma dan asalin jihar ya samu kuri’u 1,232,133 inda ya kayar da Atiku wanda ya samu kuri’u 303,056.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel