Da dumin sa: An can ana tattara kuri'u, 'yan bindiga sun tafka barna a wata jihar Arewa

Da dumin sa: An can ana tattara kuri'u, 'yan bindiga sun tafka barna a wata jihar Arewa

Wasu 'yan bindigan da ba'a san ko su waye ba mun samu labarin cewa sun kai hari a wasu kauyukan dake cikin karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto dake a Arewa maso yammacin Najeriya da daren ranar Litinin din da ta gabata.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin jaje da gwamnan jihar ta Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal yayiwa kafatanin 'yan jihar a kafafen yada labarai da safiyar ranar Talata inda yace akalla mutane 16 ne akace sun rasa ransu yayin harin.

Da dumin sa: An can ana tattara kuri'u, 'yan bindiga sun tafka barna a wata jihar Arewa
Da dumin sa: An can ana tattara kuri'u, 'yan bindiga sun tafka barna a wata jihar Arewa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Jerin jahohin da ake jiran sakamakon su yanzu

Gwamnan wanda ya nuna alhinin sa game da harin da aka kai tare da mika ta'aziyyar sa ga iyalan mamatan, ya kuma bukaci jami'an tsaron da ke jihar su kara kaimi wajen ganin sun kawo karshen rashin zaman lafiyar da jihar ke fama da shi.

Kauyukan da 'yan bindigar suka kai harin dai sun hada da Dalijan, Rakkoni da kuma Kalhu dukkanin su a karamar hukumar ta Raba inda aka ce sun yi ta harbe harben kan-mai-uwa-da-wabi yayin farmakin na su.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jahohin Arewa maso yamma da suka hada da Zamfara, Katsina, Kaduna da kuma Sokoto suna fama da rashin tsaron sakamakon hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel