Zaben 2019: Blessing Onuh ta lashe kujerar Majalisa a Otukpo/Ohimini

Zaben 2019: Blessing Onuh ta lashe kujerar Majalisa a Otukpo/Ohimini

Mun ji labari cewa Blessing Onuh, diyar Sanata David Mark tayi nasara a zaben majalisar wakilan tarayya na yankin Otukpo/Ohimini na jihar Benuwai. Blessing Onuh tayi takara ne a jam’iyyar APGA.

Zaben 2019: Blessing Onuh ta lashe kujerar Majalisa a Otukpo/Ohimini
Yarinyar Sanata Mark mai suna Blessing Onuh ta ci zabe
Asali: Depositphotos

Blessing Onuh wanda ta bijirewa Mahaifin ta, ta fito takara ne a karkashin jam’iyyar adawa ta APGA, yayin da Mahafin na ta watau Sanata David Mark yake cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP a Benuwai da kuma fadin Najeriya.

Onuh ta doke Kawun ta watau Egli Johnson Ahubi a zaben da aka yi a karshen makon da ya gabata. Johnson Ahubi yayi takara ne a karkashin jam’iyyar PDP mai mulkin jihar. Tuni dai Kawun na ta ya aika mata sakon taya ta murna.

KU KARANTA: PDP ta karbe wata kujerar Majalisa daga hannun Jam’iyyar APC

Misis B. Onuh ta sauya sheka ne daga PDP zuwa APGA bayan ta rasa tikitin takara a daf da zabe. Da yake ta taki sa’a, an yi dace ta doke sauran ‘yan takara wajen samun nasara a zaben. Wasu na ganin ta ci alfarmar Mahaifin ta ne.

‘Dan takarara PDP din da ya sha kasa, tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki ne a jihar Benuwai. Yanzu dai shi kan sa Sanata David Mark da yake majalisa tun 1999 ba zai koma kujerar sa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel