Bayan shan kaye a Kano, Kwankwaso ya aikewa masoyan sa da muhimmin sako

Bayan shan kaye a Kano, Kwankwaso ya aikewa masoyan sa da muhimmin sako

Yayin da sakamakon zabukan da aka gudanar a dukkan fadin Najeriya ke cigaba da fitowa, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da su guji tayar da hankali bayan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya.

Sanata Kwankwaso, wanda ke zaman jagoran jam'iyyar adawa ta PDP a jihar ta Kano, ya yi wannan kira ne bayan jam'iyya mai mulki ta APC ta yi nasara a kujerun majalisar dattawa da ta wakilai da ma shugaban kasa a jihar.

Bayan shan kaye a Kano, Kwankwaso ya aikewa masoyan sa da muhimmin sako
Bayan shan kaye a Kano, Kwankwaso ya aikewa masoyan sa da muhimmin sako
Asali: UGC

KU KARANTA: Sunayen wasu 'yan siyasa da suka fadi rumfar su

Ya ce za su dauki matakai na shari'a domin tabbatar da cewa rashin adalcin da aka yi musu bai dore ba.

A cewarsa, "Ina so na jawo hankalinmu cewa zaman lafiya shi ya fi komai muhimmanci; ka da wani ya dauki doka a hannunsa a kan wannan zabe.

"Muna fata mutane za su ci gaba da shirye-shirye na zaben gwamna da na 'yan majalisar dokokin jiha."

Ya kara da cewa sakamakon zaben shugaban kasa na ci gaba da nuna cewa babu tabbas kan wanda zai yi nasara har sai an kammala bayyana sakamakon.

Sanata Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa musamman a jihar Kano da su sake daura damara domin kayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Gwamna Ganduje dai ya raba gari da Sanata Kwankwaso ne tun bayan da ya hau kan mulki a 2015.

Ana zargin Gwamna Ganduje da karbar cin hanci na daloli a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel