2019: Ba zabe aka yi a Jihar Akwa-Ibom ba inji Jam’iyyar APC

2019: Ba zabe aka yi a Jihar Akwa-Ibom ba inji Jam’iyyar APC

- Jam’iyyar APC tayi tir da sakamakon zaben da ya fito daga Akwa Ibom

- APC tace akwai alamar tambaya game da nasarar da PDP ta samu a Jihar

2019: Ba zabe aka yi a Jihar Akwa-Ibom ba inji Jam’iyyar APC
APC ta nemi ayi watsi da zaben da aka yi a Akwa Ibom
Asali: Depositphotos

Mun samu labari cewa APC mai mulki ta nuna rashin amincewar ta da sakamakon zaben shugaban kasa da ya fito daga jihar Akwa-Ibom. Wani wanda ya wakilci APC wajen kididdigar kuri’u yace akwai babbar matsala da zaben.

Wakilin jam’iyyar APC a zaben na 2019, Samuel Akpan, ya fadawa ‘yan jarida cewa ba za su amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a jihar Akwa-Ibom. Wakilin na APC ya nemi INEC ta sake zabe a daukacin Jihar.

KU KARANTA: APC tace ba ta yarda da zaben da aka yi a Jihar Anambra ba

Samuel Akpan yake cewa sakamakon da INEC ta saki ya sabawa ainihin abin da ya faru a rumfunan zabe. Akpan yace ba abin da jama’a su ka zaba ba aka fitar a matsayin sakamakon zaben da aka yi a karshen makon da ya wuce.

Babban jami’in jam’iyyar ya bayyana cewa APC ba za ta dauki mataki a hannun ta ba domin akwai bukatar a zauna lafiya, don haka su kayi kira ga hukumar zabe su soke zaben da aka yi a dukkanin mazabu da gundumomi na jihar.

Jam’iyyar PDP ce tayi nasara a jihar Kudancin kasar inda Atiku Abubakar ya doke Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kananan hukumomi 28 daga cikin kananan hukumomi 31 da ake da su a jihar da jam’iyyar PDP ta ke mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel