Nasarar Okorocha: Tilasta ni aka yi na sanar da sakamako – Baturen zabe

Nasarar Okorocha: Tilasta ni aka yi na sanar da sakamako – Baturen zabe

Baturen zaben kujerar sanatan jihar Imo ta Yamma, Farfesa Ibeawuchi Innocent, ya bayyana cewar ya sanar da sunan gwamna Rochas Okorocha a matsayin wanda ya yi nasar lashe zaben kujerar sanata ne cikin halin matsin lamba.

Ya yi wannan kalami ne yayin sanar da sakamakon zaben kujerar sanatan yankin jihar Imo na yamma.

Na taba kasancewa cikin irin wannan yanayi na fuskantar matsin lambar sanar da sakamakon zabe, yanzu haka ma ga ni na sake tsinatar kai na cikin sa,” a cewae Farfesa Innocent.

Sannan ya kara da cewa, “Okorocha Anayo Rochas na jam’iyyar APC, bayan cika dukkan ka’idoji, ya samu kuri’u ma fi rinjaye, a saboda haka ya tabbata a matsayin wanda lashe zabe.”

Kamar yadda sakamakon ya nuna, jam’iyyar APC ta samu kuri’u 97,762 adadin da ya ba ta nasara a kan jam’iyyar PDP wacce ta samu kuri’u 68,117.

Nasarar Okorocha: Tilasta ni aka yi na sanar da sakamako – Baturen zabe
Rochas Okorocha
Asali: Depositphotos

Okorocha na daga cikin gwamnonin APC 5 da za su tafi majalisar dattijai bayan kammala zango biyu a kujerar gwamna.

DUBA WANNAN: Yadda sojoji su ka kwace takardun sakamako daga hannun mu – Ma’aikatan INEC a Ribas

Ragowar gwamnoni 4 su ne; Kashim Shettima na jihr Borno, Ibrahim Geidam na jihar Yobe, Ibikunle Amosun na jihar Ogun, da kuma Abdulaziz Yari na jihar Zamfara.

Shi kuwa gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, kaye ya sha a zaben da aka yi ranar Asabar, 23 ga wata, a takarar neman kujerar sanata da ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel