Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta soke zaben jihar Ebonyi, ta fadi dalili

Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta soke zaben jihar Ebonyi, ta fadi dalili

- APC a jihar Ebonyi ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka kad'a a ranar Asabar

- APC ta yi ikirarin cewa an tafka kura kura a zaben da suka hada da cin zarafin jama'a, yin barazana ga magoya bayan jam'iyyar da sauransu

- Haka zalika, ta yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta soke wannan sakamakon zabe

Jam'iyyar APC a jihar Ebonyi ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da aka kad'a a ranar Asabar. Haka zalika, ta yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta soke wannan sakamakon zabe.

Eze Nwachukwu ya bayyana matsayin jam'iyyar kan sakamakon zaben da INEC ta sanar a wani taron manema labarai na bayan zabe da ta gudanar a sakatariyar jam'iyyar da ke Abakaliki.

KARANTA WANNAN: Yanzu: Amfani da takardun bogi ya sa kotu ta tsige wani dan majalisa a Filato

Mr Nwachukwu ya yi ikirarin cewa an samu kura kura masu yawa a yayin gudanar da zaben da suka hada da dangwalawa jam'iyyu fiye da daya a takardar kad'a kuri'a guda daya, cin zarafin jama'a, tunzurawa da kuma cafke wasu jami'an APC na rumfunan zabe da kuma barazana ga mambibi da magoya bayan jam'iyyar.

Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta soke zaben jihar Ebonyi, ta fadi dalili
Babbar magana: APC ta bukaci INEC ta soke zaben jihar Ebonyi, ta fadi dalili
Asali: Depositphotos

Ya yi ikirarin cewa ba a yi amfani da na'urar tantance masu kad'a kuri'a wajen tantance masu zabe ba tare da karya dokar tsarin zabe kamar yadda INEC ta tsara a kowacce rumfar zabe.

Haka zalika shugaban jam'iyyar ya yi ikirarin cewa an aika da sakamakon zaben sanatoci da na yan majalisun wakilan tarayya na mazabar Ebonyi ta tsakiya da Ezza ta Kudu da Ikwo zuwa shelkwatar INEC ta jiha, sabanin dokar zabe akan hakan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel