Yanzu: Amfani da takardun bogi ya sa kotu ta tsige wani dan majalisa a Filato

Yanzu: Amfani da takardun bogi ya sa kotu ta tsige wani dan majalisa a Filato

- Wata kotu a Jos, ta tsige wani dan majalisar dokokin jihar Filato, Ibrahim Hassan, bayan samunsa da amfani da takardun karatu na bogi

- Mai shari'ar, Musa Kurya, a ranar Talata ya ce babu wata hujja ta cewar takardar karatun da dan majalisar ya aikawa INEC ya karbe ta daga jami'ar Jos

- Da wannan, ya bayar da umurnin cewa rantsar da Mr Saleh, domin maye gurbin korarren dan majalisar

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke da zama a Jos, ta tsige wani dan majalisar dokokin jihar Filato, Ibrahim Hassan, bayan samunsa da amfani da takardun karatu na bogi. Dan majalisar ya yi ikirarin cewa ya kammala karatun karamar diploma a bangaren Kasuwanci daga jami'ar Jos.

Sai dai, Premium Times ta ruwaito cewa magatakardar jami'ar Jos, Moday Danje, ya nisanta jami'ar daga wannan ikirari na dan majalisar, yana mai cewa sakamakon jarabar na bogi ne.

Dan majalisar da aka tsige, wanda a yanzu yake wakiltar mazabar Jos ta Arewa maso Arewa a majalisar dokokin jihar Filato, ya gurfana ne gaban kotu a shekarar 2015 bayan da Abdul Saleh ya shogar da shi kara.

KARANTA WANNAN: Dele Momodu ya shawarci Atiku: 'Ka kira Buhari tun yanzu ka taya shi murna'

Yanzu: Amfani da takardun bogi ya sa kotu ta tsige wani dan majalisa a Filato
Yanzu: Amfani da takardun bogi ya sa kotu ta tsige wani dan majalisa a Filato
Asali: Depositphotos

Mr Saleh, ya tsaya takarar fidda gwani na jam'iyyar APC a 2015 amma ya sha kasa.

Mai shari'ar, Musa Kurya, a ranar Talata ya ce babu wata hujja ta cewar takardar karatun da dan majalisar ya aikawa INEC ya karbe ta daga jami'ar Jos. Mr Kurya ya ce bisa hujja ta rubuce da kuma ta baki da magatakartar jami'ar ya gabatarwa kotu, ta tabbata cewa takardun karatun da Mr Hassan ya gabatarwa INEC a 2015 na bogi ne.

Mai shari'ar ya amsa gaba daya rokon da Mr Saleh ya gabatarwa kotun, tare da yanke hukunci cewa Mr Hassan bai cancanci zama dan majalisa ba. Da wannan, ya bayar da umurnin cewaa rantsar da Mr Saleh wanda ya zo na biyu a zaben fitar da gwani na jam'iyyar, domin maye gurbin korarren dan majalisar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel