El-Rufa'i ya gana da Buhari a kan kisan mutane a Kajuru

El-Rufa'i ya gana da Buhari a kan kisan mutane a Kajuru

A yau, Talata, ne shuagaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nsir El-Rufa’i, su ka yi wata ganawar sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa cewar majiyar sa ta tabbatar ma sa da cewar gwamnan zai yi amfani da ganawar ta su domin yi wa shugaban kasa bayani a kan sabon harin da aka sake kai wa a kan al’ummar kauyukan kananan hukumomin Kajuru da Kachia.

A wata sanarwa da kakakin sa, Samuel Aruwan, ya fitar da safiyar yau, Talata, El-Rufa’i ya tabbatar da cewar an sake kai hari a wasu kauyuka da ke karkashin kananan hukumomin Kajuru da Kachia da ke jihar Kaduna.

A yau, Talata, ne gwamnatin jihar Kaduna ta samu labarin abin takaici na kai sabon hari a kananan hukumomin Kajuru da Kachia.

El-Rufa'i ya gana da Buhari a kan kisan mutane a Kajuru
El-Rufa'i da Buhari
Asali: Twitter

“Gwamnati ta yi Alla-wadai da wannan hari da duk wani yunkurin tayar da hankali. Mu na kira da mazauna yankunan da su bawa kokarin mu na tabbatar da zaman lafiya a yankin hadin kai," a cewar sanarwar gwamnatin.

DUBA WANNAN: Nasarar Okorocha: Tilasta ni aka yi na sanar da sakamako – Baturen zabe

NAN ta rawaito cewar ba ta samu bayanin sakamakon ganawar Buhari da El-Rufa’i ba wacce ta dauki tsawon kasa da sa’a guda.

A ranar 19 ga watan Fabarairu ne El-Rufa’i ya bayyana wa manema labarai cewar adadin wadanda su ka mutun a harin da aka kai wasu rugagen Fulani a karamar hukumar Kajuru a daren ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu, ya karu zuwa 130 daga 66.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel