An kama wata malama da laifin fyade ga wata yarinya a jihar Ikko

An kama wata malama da laifin fyade ga wata yarinya a jihar Ikko

- Anci gaba da ajjiye wata mata a gidan kason Kirikiri

- An kamata da laifin tarawa da wata yarinya yar shekara Hudu

- Yarinya tana kukan cewa tanajin ciwo a bum bum dinta

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Source: UGC

A ranar Talata ne wata kotu mai zaman ta a Ikeja ta bada umarnin a cigaba da ajjiye wata malamar makaranta yar kimanin shekaru 29 mai suna Adejuyigbe Moni wadda aka kama tana tarawa da wata yarinya yar shekara Hudu ta hanyar sanya mata hannu a gaban ta.

Alkalin kotun Mrs Olufunke Sule Amzat ta bada umarnin a cigaba da rike wannan mata a gidan kason Kirikiri dake jihar Legas.

Wanda ya shigar da karar Mr Benson Emuerhi ya bayyanawa kotu cewa wadda ake tuhumar ta aikata wannan abu ne a ranar 13 ga watan Junairu a harabar Covenants tecno kids discovery center dake lamba 14,Akeem-oke street Igando jihar Legas.

Yace an mika wannan case zuwa gender section dake karkashin hukumar yan sandan jihar Legas wanda mahaifin yarinyar ya shigar a madadin ta.

Ya kara da cewa yarinyar tana ta yiwa iyayanta kukan cewa tanajin zafi a bum bum din ta.

Yarinyar tace"malamar ajinsu ce ta sanya mata hannu a gabanta wanda ya janyo mata jin zafin".

Iyayen yarinyar sun garzawa zuwa hukumar makarantar inda suka shigar da korafi.

Wadda ake tuhumar ta kalubalanci wannan abu.

Hakkewa kananun yara ya sabawa doka mai lamba 261 na dokokin jihar Legas idan kuma aka kama mutum da aikata wannan laifi zai fuskanci hukuncin tsarewa a gidan kaso na tsayin shekaru Bakwai.

An dage sauraran wannan kara zuwa 11 ga watan Afrilu da zamu shiga.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel