Jamiyyar APC tayi babban rashi bayan da aka kada Sanatan ta a jihar sa ta Benue

Jamiyyar APC tayi babban rashi bayan da aka kada Sanatan ta a jihar sa ta Benue

- Sanata George Akume ya rasa kujerar sa

- An bayyana Emmanuel Oker Jev a matsayin wanda yayi nasara

- Jev ya na jam'iyar PDP ya samu kuri'u 157,726 inda ya doke sanata kuma jagoran jam'iyar APC a jihar tasu

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Asali: Depositphotos

Sanata George Akume ya rasa kujerar sa ta sanata yayin da aka bayyana Emmanuel Orker Jev a matsayin wanda yayi nasarar dare kujerar ta jihar Benue.

Jev na jam'iyar PDP ya samu kuri'u 157,726 inda ya doke sanata mai ci a yanzu kuma jagoran jam'iyar APC a jihar wanda ya samu kuri'u 115,422.

DVC na jami'ar Agriculture dake Makurdi Professor Nicodemus Ochani yace ba za'a kansile zaben ba.

Shuaib Ishember itace mace daya tilo data nemi wannan kujera a jam'iyar JMPP ta samu kuri'u 51 yayin da ragowar yan takarar suma suka samu abinda suka samu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel