Yanzu-yanzu: Hukumar Soji ta damke jami'in INEC dake yiwa Gwamna Wike aiki

Yanzu-yanzu: Hukumar Soji ta damke jami'in INEC dake yiwa Gwamna Wike aiki

Hukumar sojin Najeriya ta damke akalla mutane takwas dake da hannu wajen tayar da tarzoma a zaben da aka gudanar ranan Asabar a jihar Ribas.

Yayinda hukumar ke bayyana yan barandan a garin Fatakwal ranan Talata, kakakin hukumar, Sagir Musa, ya ce yan barandan sun bayyana cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, suke yiwa aiki.

Yace yan barandan sun sanya kaya kaman ma'aikatan hukumar INEC kuma suka kawo matsala wajen zabe.

Kana ya tabbatar da cewa sun samu faifan odiyon maganar yan barandan da gwamnan.

An bayyanasu a hedkwatan hukumar Soji dake jihar kuma an kai inda suka ajiye motar gidan gwamnatin jihar wacce sukayi amfani da ita.

Mun kawo muku cewa a yau, Talata, ne shuagaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nsir El-Rufa’i, su ka yi wata ganawar sirri a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa cewar majiyar sa ta tabbatar ma sa da cewar gwamnan zai yi amfani da ganawar ta su domin yi wa shugaban kasa bayani a kan sabon harin da aka sake kai wa a kan al’ummar kauyukan kananan hukumomin Kajuru da Kachia.

A wata sanarwa da kakakin sa, Samuel Aruwan, ya fitar da safiyar yau, Talata, El-Rufa’i ya tabbatar da cewar an sake kai hari a wasu kauyuka da ke karkashin kananan hukumomin Kajuru da Kachia da ke jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel