Jami’an EFCC sun aikawa AGF takarda ya cafko Alison-Madueke

Jami’an EFCC sun aikawa AGF takarda ya cafko Alison-Madueke

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta rubuta takarda zuwa ga Alkalin wani kotu da ke Abuja tana nema a dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya.

Jami’an EFCC sun aikawa AGF takarda ya cafko Alison-Madueke
EFCC na zargin Diezani Alison-Madueke da wawurar dukiyar kasa
Asali: Depositphotos

EFCC tana bukatar a tattaro tsohuwar minister harkokin man fetur na Najeriya, Diezani Alison-Madueke. Tuni dai hukumar ta mikawa Ministan shari’a na Najeriya wannan bukatar ta ta domin a binciki tsohuwar Ministar kasar.

A jiya ne aka shriya yin zama a babban kotun tarayya da ke cikin Garin Apo a Abuja domin cigaba da shari’ar da ake yi da Diezani Alison-Madueke, da kuma wani yaron ta Jide Omokore wanda EFCC ta ke zargi da laifin satar kudi.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta sha mugun kayi a hannun Buhari a Jihar Borno

A shekarar bara ne kotu ta bada umarni a kawo mata Diezani Madueke gaban ta domin ayi shari’a. Sai dai har yanzu Madam Alison-Madueke, tana kasar Ingila, ta ki shigowa Najeriya domin wanke kan ta daga dukkanin wani zargi.

Bayan an nemi tsohuwar Ministar kasar an rasa ne, Lauyan da ke kara watau Faruk Abdullahi ya fadawa kotu cewa tuni su ka aika takarda zuwa ga Ministan shari’an Najeriya domin a fatattako keyar wanda ake zargin zuwa gaban kuliya.

Kwanan nan ne kuma Lauyan na EFCC yake cewa za su aikawa Jide Omokore sammacin kotu. Alkali Valentine Ashi y adage karar zuwa 22 ga Watan Mayu domin a cigaba da shari’a. Ana sa rai kowa ya hallara zuwa wannan lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel