Yadda sojoji su ka kwace takardun sakamako daga hannun mu – Ma’aikatan INEC a Ribas

Yadda sojoji su ka kwace takardun sakamako daga hannun mu – Ma’aikatan INEC a Ribas

Wasu ma’aikatan hukumr zabe ta kasa (INEC) a jihar Ribas sun bayyana cewar sojoji sun yi ma su dirar mikiya a kananan hukumomin Emohua da Ikwerre tare da kwace takardun rubuta sakamakon zaben shugaban kasa da ‘’yan majalisar tarayya.

Ma’aikatan sun shaidawa manema labarai da m su sa-ido a zabe cewar wani tsohon kwamishina a lokacin mulkin Rotimi Amaechi ne ya jagoranci kutsen da sojoji su ka yi a cibiyar tattara sakamako da ke karamar hukumar Emohua.

Uwargida Merry Efeture, baturiyar zabe a karamara hukumar Ekwerre, ta bayyana cewar ba a tattara sakamakon zabe a karamar hukumar ba saboda kusten da sojojin su ka yi a cibiyar tattara sakamako da ke Isiokpo.

Tsakanin 7 zuwa 8 na daren ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, sojoji sun yi dirar mikiya a cibiyar mu tattara sakamako da ke Isokpo, su ka kori dukkan ma’aikatan wucin gadi da ke wurin domin gabatar da sakamakon zabe a mazabu daban-daban da su ka yi aiki. Mu na da shaida a kan faruwar hakan domin mun nadi duk abinda ya faru.

Yadda sojoji su ka kwace takardun sakamako daga hannun mu – Ma’aikatan INEC a Ribas
Nyesom Wike; gwamnan jihar Ribas
Asali: Depositphotos

“Ba mu samu tattara sakamakon zaben da aka yi ba. Na samu damar karbar dukkan sakamakon zabe daga hannun ma’aikatan mu na wucin gadi kuma na mika su zuwa ofishin INEC na jiha,” a cewar uwargida Efeture.

Ta kara da cewar sojojin sun katse gabatar da sakamakon zaben ta hanyar yin harbin iska kafin daga bisani su kwace kayayyakin zaben.

A nasa bangaren, baturen zabe a karamar hukumar Emohua, Kenneth Etah, ya zargi dakarun soji da katse tattara sakamakon zabe ta hanyar firgita su da harbin bindiga.

DUBA WANNAN: Ka kira Buhari ka taya shi murna – Dele Momodu ya bawa Atiku shawara

Kenneth ya ce, “ba ni da wani sakamakon zabe da zan gabatar dcaga karamar hukumr Emohua saboda ba mu samu damar tattara sakamon zabe ba saboda yawaitar harbe-harbe da sojoji ke yi. An dauki kimanin sa’a guda su na ta harbi kafin daga bisani jami’an tsaro su samu damar tserar da mu.

“Bayan jami’an tsaro sun rako ni ofishi na da misalin karfe 5:00 na safe domin daukan sakamakon zabe sai na samu an balle kofa an kwashe takardun sakamakon zaben.

Tun a ranar Asabar rahotanni su ka bayyana cewar an samu barkewar rikici a jihar Ribas yayin da jama’a su ka fita domin kada kuri’un su a zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel