Sakamakon zabe: Allah ne kadai ya san abinda zai iya faruwa - Kwankwaso

Sakamakon zabe: Allah ne kadai ya san abinda zai iya faruwa - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana sadudarsa game da sakamakon zaben dake fita daga bakunan turawan zabe na hukumar INEC, don haka yayi kira ga magoya bayansa dasu kwantar da hankulansu.

Kwankwaso ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 26 ga watan Feburairu, inda ya tabbatar ma magoya bayansa cewa zasu dauki matakin daya dace kamar yadda doka ta tanada, sa’annan yayi kira a garesu da kowa ya sake shiri domin tunkarar zaben gwamnoni.

KU KARANTA: Daga fadar gwamnati zuwa majalisar dattawa: Jerin wasu gwamnoni guda 6 da kakarsu ta yanke saka

“Mutanen Kano, Assalamu Alaikum Warahmatullahi ta’ala wa barakatuhu, ina godiya ga Allah daya nuna mana wanna zabe na shugaban kasa da Sanatoci da yan majalisu na tarayya wanda aka yi ranar 23 ga watan Feburairu a wannan jaha tamu ta Kano da ma kasa baki daya.

“Zabe muna iya cewa an yi shi lafiya, kuma an gama lafiya, kuma musamman mu yan jam’iyyar PDP, ga irin abinda suka faru na rashin jin dadi, amma ina fata mutane zasu kwantar da hankalinsu domin zamu dauki matakai a wuraren daya kamata, wanda doka ta tanada.

“Ina so na jawo hankalinmu da cewa zaman lafiya shi yafi komai muhimmanci, kada wani yace zau dauki doka a hannunsa a wannan lokaci saboda wannan zabe, ina fata mutane zasu cigaba da abubuwan daya kamata su yi na shirye shiryen zabe na gwamna da nay an majalisun jihohi.” Inji shi.

Sai dai Kwankwaso yace duba da sakamakon shugaban kasa da ake samu daga jihohi, inda APC ke cin wasu, PDP ke cin wasu, don haka yace Allah ne kadai ya san abinda zai iya faruwa a ciki.

Kwankwaso ya ja hankalin magoya bayansa da kada su dauki doka a hannunsu a sakamakon rashin nasara ko samun nasara, domin a tabbatar da zaman lafiya, kuma suma jam’iyyun hamayya su yi kira ga nasu magoyan.

Daga karshe Kwankwason yayi addu’ar Allah ya zaunar da jahar Kano lafiya, Ya cigaba da kara zaman lafiya da kwanciyar hankali a jahar, tare da kasa Najeriya gabaki daya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel