Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa a Adamawa

Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a ranar Talata, 26 ga watan Fabrairu ta kaddamar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu a jihar Adamawa.

Atiku wanda ya kasance dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya lashe zabe hankali kwance a jiharsa da kuri’u 410,266.

Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa a Adamawa
Yanzu Yanzu: INEC ta kaddamar da Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa a Adamawa
Asali: Original

A cewar INEC babban abokin adawa Atiku, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri’u 378,078.

Legit.ng ta kula cewa Atiku ya kasance mai rike da mukamin sarauta a jihar. Shine Wazirin Adamawa a yanzu bayan ya barwa dansa mukaminsa na baya wato Turakin Adamawa.

Ga sakamakon da INEC ta saki:

KU KARANTA KUMA: Yanzu Saraki zai tuna cewa akwai Allah – Ndume yayi murnar faduwar Shugaban majalisar dattawa

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa wasu daga cikin mazauna birnin Sokoto sun mamaye titunan garin a ranar Talata inda suka rika tika rawa da wakoki domin murnar nasarar da 'yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka samu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Jam'iyyar APC ta lashe dukkan kujerun sanata guda uku na jihar inda ta yi nasara babban abokiyar hammayarta wato PDP. Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 490,333 a jihar inda Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 361,604.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel