Daga fadar gwamnati zuwa majalisar dattawa: Jerin wasu gwamnoni guda 6 da kakarsu ta yanke saka

Daga fadar gwamnati zuwa majalisar dattawa: Jerin wasu gwamnoni guda 6 da kakarsu ta yanke saka

Tun bayan kammala kada kuri’u a babban zaben Najeriya daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu ne aka fara tattara alkalumman sakamakon zaben daga kowace rumfa, mazaba, karamar hukuma, jaha da ma kasa baki daya, tare da kidayarsu.

Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu an fara samun tabbatattu kuma sahihan sakamakon zabukan da suka gudana, inda yan siyasa da dama da suka tsaya takara sun fara sanin matsayinsu, walau sun samu nasara ko kuma akasin haka.

KU KARANTA: Sakamakon zabe: Tsofaffin gwamnonin Najeriya 7 da suka lashe zaben Sanata

Daga fadar gwamnati zuwa majalisar dattawa: Jerin wasu gwamnoni guda 6 da kakarsu ta yanke saka
Gwamnoni Sanatoci
Asali: UGC

Anan mun kawo muku jerin wasu gwamnonin Najeriya ne da zasu zarce zuwa majalisar dokoki ta kasa kai tsaye, bayan sun samu nasara a yayin zaben Sanatoci a mazabuncu, wanda hakan ke nufin zasu koma wakiltar al’ummominsu a majalisar dattawa, ma’ana sun zama Sanata wane da Sanata wane.

Ga wasu daga cikin gwamnonin, da kuma kuri’un da suka yi amfani dasu wajen lallasa abokan karawarsu masu karfin hali, domin kuwa karawa da gwamna mai ci a siyasar Najeriya sai mai karfin hali.

- Abdul Aziz Yari na jahar Zamfara ya lashe zabe da kuri’u 153,626, yayin da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Lawal Hassan ya samu 69,293. Zai wakilci mazabar Zamfara ta yamma.

- Kashim Shettima na jahar Borno ya lashe zabe da kuri’u 342,898, yayin da abokin karawarsa na jam’iyyar PDP, Abba Aji ya samu kuri’u 75,506. Zai wakilci mazabar Borno ta tsakiya.

- Ibrahim Gaidam na jahar Yobe ya lashe zabe da kuri’u 139,277, yayin da abokin karawarsa na jam’iyyar PDP Tata Abbagana ya samu kuri’u 18,059. Zai wakilci mazabar Yobe ta gabas.

- Ibikunle Amosun na jahar Ogun ya lashe zabe da kuri’iu 88,110, yayin da abokiyar bugawarsa daga jam’iyyar ADC, Titi Oseni Gomez ta samu kuri’u 37,101. Zai wakicli mazabar Ogun ta tsakiya.

- Tanko Al-Makura na jahar Nassarawa ya lashe zabe da kuri’u 113,156, yayin da abokin karawarsa na jam’iyyar PDP, Suleiman Adokwe ya samu kuri’u 104, 495. Zai wakilci mazabar Nassarawa ta kudu.

- Sai kuma gwamnan jahar Imo Rochas Okorocha wanda shi ke kan gaba a kirgen da ake yi na sakamakon zaben Sanatan mazabar Imo da yamma, inda ya samu kuri’u 97,762, yayin da abokin hamayyarsa, Jones Onyereri na PDP ya samu 68,117.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel