Yanzu Saraki zai tuna cewa akwai Allah – Ndume yayi murnar faduwar Shugaban majalisar dattawa

Yanzu Saraki zai tuna cewa akwai Allah – Ndume yayi murnar faduwar Shugaban majalisar dattawa

- Sanata Ali Ndume yace yanzu Saraki zai tuna cewa akwai Allah bayan kaye da ya sha a zaben sanata

- Ndume yayi matukar farin ciki da wannan faduwa na Saraki

- Ya yi zargin cewa Saraki na ji takar ubangiji a lokacin mulkinsa a matsayin Shugaban majalisar dattawa don haka Allah ya nuna masa iyakarsa

Sanata mai wakiltan yankin Borno ta Kudu a majalisar dokokin kasar, Sanata Muhammadu Ali Ndume yayi murnr faduwar Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a zaben ranar Asabar da ya gudana.

“Kila wannan zai tuna wa Saraki cewa akwai Allah,” Sanata Ndume wanda ya lashe kujerarsa na sanata ga manema labarai a yammacin ranar Litinin a Maiduguri.

Yanzu Saraki zai tuna cewa akwai Allah – Ndume yayi murnar faduwar Shugaban majalisar dattawa
Yanzu Saraki zai tuna cewa akwai Allah – Ndume yayi murnar faduwar Shugaban majalisar dattawa
Asali: Facebook

Sanata Ndume yace Saraki na ji takar ubangiji a lokacin mulkinsa a matsayin Shugaban majalisar dattawa inda yace, “Da zaran ka fara yi tamkar Ubangiji, sai Allah ya nuna maka iyakarka, Saraki ya yi tamkar Ubangiji, sannan kum ga yadda Allah yayi da shi.

KU KARANTA KUMA: KAI TSAYE: Sakamakon zaben shugaban kasan Najeriya

Yace: “Saraki na daukar abubuwa da rashin kima, wannan shine makomar duk wanda bai daukar abubuwa da muhimmani.”

A halin da ake ciki, Shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki, ya taya wadanda suka lashe zabe a jihar Kwara da ma kasar baki daya murnar nasarar da suka samu, yayin da a hannu daya kuwa ya ce an tafka kura kurai a zaben jihar musamman na mazabarsa ta Kwara ta Kudu.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, Dr Bukola Saraki wanda ya yi takara karkashin jam'iyyar PDP a zaben ranar Asabar da ya gudana ya rasa kujerarsa ta majalisar dattijai ga tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Dr Ibrahim Oloriegbe na jam'iyyar APC.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel