Majalisar dattijai ta dawo, ko dattijo Saraki ya sami halarta?

Majalisar dattijai ta dawo, ko dattijo Saraki ya sami halarta?

- Majalisar dattawa zata dawo da cikakken zaman zauren a ranar 12 ga watan maris

- Ta dage dawowa ranar 26 ga watan fabrairu sakamakon rashin samun karancin yawan mahukuntan sun dawo

- Mahukuntan basu dawo bane sakamakon wasu basa gari kuma basu riga sun san makomar zabubbukan yankin su

Majalisar dattijai ta dawo, ko dattijo Saraki ya sami halarta?
Majalisar dattijai ta dawo, ko dattijo Saraki ya sami halarta?
Asali: UGC

Majalisar dattawa zata dawo da cikakken zauren ta q ranar talata amma ta daga sakamakon rashin cikar mafi karancin yan majalisar da ake bukata.

Wannan ne taro na farko da majalisar zatayi bayan zaben shugaban kasa da majalisar dattawa.

An tsara dawowar mahukuntan ne a ranar 19 ga watan Fabrairu amma aka dage zuwa 26 ga watan Fabrairu sakamakon dage zaben da akayi.

Daga dawowar, shugaban majalisar Ahmad Lawan ya dage zaman sakamakon wadanda ke majalisar basu kai karancin yawan mutanen da ake bukata don zaman majalisar ba.

GA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga Adamawa, Borno da Yobe a Arewa maso gabas ya zuwa yanzu

Yayi bayanin cewa yayin da wasu daga cikin ya majalisar basa gari kuma basu samu sakamakon zaben sanatocin yankin su ba, wasu kuma na tabbatarwa da cewa aiyukan zabe a yankin su ya tafi kalau.

Daga nan ne ya dage zaman majalisar zuwa 12 ga watan Maris bayan zaben gwamnoni da na majalisar jiha.

Sanatan Abuja, Philip Aduda shi ya goyi bayan dage zaman.

An samu sanatoci kusan takwas a babban zauren majalisar. Sun hada da Bukola Saraki, wanda ya jagoranci zaman. Mataimakin kakain majalisar Ike Ekweremadu, Olusola Adeyeye da Andrew Uchendu ma duk suna nan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel