Dele Momodu ya shawarci Atiku: 'Ka kira Buhari tun yanzu ka taya shi murna'

Dele Momodu ya shawarci Atiku: 'Ka kira Buhari tun yanzu ka taya shi murna'

Dele Momodu, mawallafin mujallar Ovation, ya bukaci dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya kira shugaban kasa Muhammadu Buhari tun yanzu domin taya shi murnar lashe zaben shugaban kasar.

Momodu a cikin jerin gwanon rubuce rubucen da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata, ya roki Atiku da ya sanya Nigeria akan saman komai, tare da daukar kaddara ta shan kaye ba tare da la'akari da jin ko an cuce shi a zaben shugaban kasar da aka kad'a a ranar Asabar din da ta gabata ba.

Rubuce rubucen na sa sun biyo bayan sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar na jihohi 12, inda shugaban kasa Buhari ke kan gaba.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun sake kai sabon hari a Kaduna, sun kashe mutane da dama

Dele Momodu ya shawarci Atiku: 'Ka kira Buhari tun yanzu ka taya shi murna'
Dele Momodu ya shawarci Atiku: 'Ka kira Buhari tun yanzu ka taya shi murna'
Asali: Depositphotos

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel