Cin zaben APC: Dubban al'umma sun mamaye titunan Sokoto

Cin zaben APC: Dubban al'umma sun mamaye titunan Sokoto

Wasu daga cikin mazauna birnin Sokoto sun mamaye titunan garin a ranar Talata inda suka rika tika rawa da wakoki domin murnar nasarar da 'yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka samu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Jam'iyyar APC ta lashe dukkan kujerun sanata guda uku na jihar inda ta yi nasara babban abokiyar hammayarta wato PDP.

Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 490,333 a jihar inda Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 361,604.

DUBA WANNAN: Zabe: Sakamako daga jihohin Sokoto, Kebbi da Jigawa

Cin zaben APC: Dubban al'umma sun mamaye tittunan Sokoto
Cin zaben APC: Dubban al'umma sun mamaye tittunan Sokoto
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya lashe zabe a kananan hukumomi 19 da ke jihar yayin da Atiku ya lashe zabe a kananan hukumomi guda hudu na jihar.

Sanata mai wakiltan Sokoto ta Arewa mai ci yanzu, Aliyu Wamakko na jam'iyyar APC ya yi nasarar lashe zabe na cigaba da kasancewa a kujerarsa inda ya doke abokin hammayarsa tsohon sanata Ahmed Maccido na PDP da fiye da kuri'u 34,000.

Wamakko ya samu kuri'u 172,980 yayin da shi kuma Maccido ya samu kuri'u 138,922.

Sanata Ibrahim Gobir na jam'iyyar APC shima ya yi nasarar cigaba da kasancewa a kan kujerarsa na Sokoto ta Gabas inda ya samu kuri'u 170,665 ya doke kakakin majalisar jihar Sokoto mai ci a yanzu, Alhaji Salihu Maidaji na PDP wanda ya samu kuri'u 140,322.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan harkokin sojoji, Sanata Ibrahim Danbaba na PDP ya rasa kujerarsa ga sabon shiga, Alhaji Shehu Tambuwal na jam'iyyar APC.

Shehu Tambuwal ya samu kuri'u 134,224 yayin da shi kuma Danbaba ya samu kuri'u 112,546.

Bala Abubakar III dan majalisar wakilai na yanzu mai wakiltar Sokoto ta Arewa/Kudu ya lashe zabe da kuri'u 71,486.

Abubakar III ya doke babban abokin hammayarsa, Abubakar Abdullahi na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 52,148.

Sanata Aminu Shehu Shagari mai wakiltar Shagari/Yabo na jam'iyyar PDP ya sha kaye a hannun Umar Abubakar na jam'iyyar APC. Abubakar ya samu kuri'u 33,193 shi kuma Shagari ya samu kuri'u 24,932.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel