Zaben 2019: Atiku ya buga Buhari da kasa a jihar Anambra

Zaben 2019: Atiku ya buga Buhari da kasa a jihar Anambra

Kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta bayar da shaida a yau Talata, mun samu cewa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi nasara a jihar Anambra yayin bayayyan sakamakon babban zaben kasa.

A yayin da a yau Talata hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ke ci gaba da bayyana sakamakon babban zabe, mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari bugun Dawa a jihar Anambra.

Hoton yadda ta kaya tsakanin Buhari da Atiku daga allon hedikwatar INEC a garin Abuja
Hoton yadda ta kaya tsakanin Buhari da Atiku daga allon hedikwatar INEC a garin Abuja
Asali: Original

Hoton yadda ta kaya tsakanin Buhari da Atiku daga allon hedikwatar INEC a garin Abuja
Hoton yadda ta kaya tsakanin Buhari da Atiku daga allon hedikwatar INEC a garin Abuja
Asali: Original

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Babban alkalin zabe reshen jihar kuma shugaban jami'ar nazarin noma ta jihar Abia, Farfesa Francis Ogbonnaya Otunta, shine ya bayar da shaidar hakan a yau Talata cikin hedikwatar hukumar zabe da ke garin Abuja.

Farfesa Otunta yayin zayyana sakamakon zaben jihar Anambra ta Kudu maso Kudancin kasar nan kuma mahaifa ga dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Peter Obi, ya ce, yayin Buhari ya sha kasa da kimanin kuri'u 33,298, Atiku ya taki nasara da kuri'u 524,738.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, baya ga jihar Anambra, Wazirin Adamawa ya kuma lallasa shugaban kasa Buhari a jihohin Adamawa, Edo da Ebonyi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel