Da duminsa: Saraki ya yi korafi kan shan kaye amma ya taya wadanda suka yi nasara murna

Da duminsa: Saraki ya yi korafi kan shan kaye amma ya taya wadanda suka yi nasara murna

Shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki, ya taya wadanda suka lashe zabe a jihar Kwara da ma kasar baki daya murnar nasarar da suka samu, yayin da a hannu daya kuwa ya ce an tafka kura kurai a zaben jihar musamman na mazabarsa ta Kwara ta Kudu.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, Dr Bukola Saraki wanda ya yi takara karkashin jam'iyyar PDP a zaben ranar Asabar da ya gudana ya rasa kujerarsa ta majalisar dattijai ga tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar, Dr Ibrahim Oloriegbe na jam'iyyar APC.

KARANTA WANNAN: Tunda nike a rayuwata, ban taba shan kwaya ba - CP Wakili

Da duminsa: Saraki ya yi korafi kan shan kaye amma ya taya wadanda suka yi nasara murna
Da duminsa: Saraki ya yi korafi kan shan kaye amma ya taya wadanda suka yi nasara murna
Asali: Depositphotos

An sanar da sakamakon mazabar ne a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ke yankin Madate, Adewole Ilorin, ta bakin jami'in tattara sakamakon zabe na mazabar Kwara ta tsakiya, Farfesa Olawole Olatunbosun na jami'ar Ilorin.

Ga yadda sakamakon zaben ya kasance:

Ilorin west

APC 51,531

PDP 30,075

Ilorin East

APC 30,014

PDP 14,654

Ilorin South

APC26,331

PDP 13,013

Asa

APC 15932

PDP 11252

Sai dai Saraki, a cikin wata sanarwa, ya ce: "Duk da cewa an samu matsaloli yayin gudanar da zaben, ina taya wadanda suka lashe zaben murnar nasarar da suka samu."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel