INEC ta soke zaben mutum 55,000 saboda injin tantance katin masu zabe

INEC ta soke zaben mutum 55,000 saboda injin tantance katin masu zabe

- Mai mika sakamakon zabe na jihar Ebonyi, ya sanar da soke kuri'u 54,668 a jihar

- Jam'iyyar PDP ce ta lashe jihar da kuri'u 258,575

- An soke kuri'un ne sakamakon matsalar card reader a sassan jihar

INEC ta soke zaben mutum 55,000 saboda injin tantance katin masu zabe
INEC ta soke zaben mutum 55,000 saboda injin tantance katin masu zabe
Asali: UGC

CO din hukumar zabe mai zaman kanta reshen jihar Ebonyi, Farfesa Chukwuemeka Eze ya sanar a Abuja a ranar talata cewa an soke kuri'u 54,668 a jihar sakamakon matsalolin da suka danganci card reader.

Eze, wanda shine shugaban jami'ar tarayya ta fasaha dake Owerri ya bayyana hakan yayin bada bayani akan sakamakon zabe na kananan hukumomi 13 na jihar da yayi a cibiyar bada sakamakon zabe ta kasa dake Abuja.

GA WANNAN: An dawo da 'yan Najeriya 166 daga Libya, an kamo masu kai su su bautar su biyu

Kamar yanda ya fada, "jimillar wadanda sukayi rijistar katin zabe sun kai 1,392,931; masu zabe 391,747 ne aka tantance; kuri'u 379,394 aka kada inda kuma aka samu kuri'u 359,131 masu amfani, sai kuri'u 20,263 da suka lalace a kananan hukumomi 13 na jihar.

Eze yace jam'iyyar PDP ta samu 258,575 kuri'u, jam'iyyar APC ta samu kuri'u 90,726 yayin da AAC ta samu kuri'u 205.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya dage sauraron sakamakon zuwa karfe 10 na safe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel