2019: An yi coge a zaben Jihar Anambra inji Wakilin APC Ngige

2019: An yi coge a zaben Jihar Anambra inji Wakilin APC Ngige

Mun ji labari cewa Ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige yana barazanar shiga kotu da hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC bayan ganin yadda jam’iyyar APC ta sha kashi a jihar Anambra.

2019: An yi coge a zaben Jihar Anambra inji Wakilin APC Ngige
Ngige yace ba su yarda da sakamakon Garuruwan Idemili ba
Asali: UGC

Jam’iyyar PDP ce ta samu gagarumar nasara a jihar Anambra a zaben shugaban kasa. Atiku Abubakar ya tashi da kuri’u 487, 550 ne yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya samu kuri’a 31, 452 a jihar da ke Kudancin Najeriya.

Chris Ngige wanda shi ne Wakilin APC a jihar ya nuna cewa bai amince da sakamakon da INEC ta fitar ba. Ngige yake cewa bai amince da sakamakon zaben da aka fitar daga yankin Idemili ba, yana ganin INEC tayi masu coge.

KU KARANTA: Ifeanyi Ubah ya tika ‘Yan gidan Ubah da kasa a zaben Sanatan Anambta

Tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana cewa adadin kuri’un da hukumar INEC ta bayyana cewa an samu, bai yi daidai da sakamakon da aka fitar a akwatin mazabar ba. Wannan ya sa Ngige ya nemi a soke kaf sakamakon yankin.

Wakilin zaben na Muhammadu Buhari yayi wa INEC barazana cewa idan har ba ta soke zaben garin Idemeli ba, zai tafi kotu domin gaskiya tayi aiki. Ngige ya zargi INEC da sabawa dokar zabe da kin amfani da na’urar aikin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel