Kurunkus: Dukkan jahohi sun gabatar da sakamakon zaben su ga INEC
Yayin da aka shiga rana ta biyu na bayyana sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata, kawo yanzu jahohi ne ke ta tururuwa suna bayyana sakamako zaben su a gaban shugaban hukumar zabe ta kasa, INEC.
Hukumar dai ta INEC ta sha fadawa 'yan kasa cewa su guji bayyana sakamakon zabe idan ba su ne suka fada ba domin sune kawai a hukumance ya kamata su ayyana.

Asali: UGC
KU KARANTA: Buhari ya kama hanyar lashe zabe
Haka zalika yanzu dai shugaban kasar Najeriya kuma wanda ya shiga takarar tazarce a jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari ne ya ke kan gaba.
Haka ma dai kawo yanzu dukkan jahohin tarayyar Najeriya sun gama gabatar da sakamakon zabukan da suka gudana a jahohin su 36 tare da babban birnin tarayyar Najeriya.
Yanzu haka dai ana sa ran hukumar zaben ta sanar da matsayar ta sannan kuma ta sanar da wanda ya lashe zabe shugaban kasa.
Ga dai dukkan sakamakon zaben nan daga jahohi kamar yadda hukumar INEC ta sanar:
Asali: Legit.ng