Ka rungumi kaddara kawai - Dele Momodu ya bawa Atiku shawara

Ka rungumi kaddara kawai - Dele Momodu ya bawa Atiku shawara

Mawallafin jaridar ‘Ovation Magazine’ kuma daya daga cikin fitattun magoya bayan dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shawarce shi da ya kira shugaba Buhari, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, a waya ya taya shi murnar samun nasara a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Mista Momodu, fitacce a dandalin sadarwar zamani, ya bayar da shawarar ne da safiyar yau, Talata, a daidai lokacin da hukumar zabe ta kasa (INEC) ke cigaba da karbar skamakon zabe daga jihohin Najeriya.

Da ya ke bawa Atiku shawara a shafin san a (@delemomodu), Mista Momodu ya ce ya san cewar Atiku zai tuntubi shugabancin jam’iyyar PDP da iyalinsa kafin ya kira Buhari. Ya kara da cewar yin hakan zai kawo zaman lafiya da kuma Karin kim ga Atiku.

A cewar Mista Momodu, “Ya mai girma Waziri, a matsayin ka na mai imani, na san cewar yarda cewaer Ubangiji ke bayar wa ko krbar mulki. Ka yi rawar gani. Kar ka ji nauyin kiran shugaba Buhari domin taya shi murna. Hakan ba zai rage ka da komai ba.”

Ka kira Buhari ta taya shi murna – Dele Momodu ya bawa Atiku shawara
Dele Momodu da shugaba Buhari
Asali: UGC

Mista Momodu na daga cikin jama’ar da su ka yi wa Atiku yakin neman zabe kuma su ka bayyana cewar su na da yakinin cewar zai lashe zaben shugaban kasa, musamman saboda gazawar gwamnati mai ci a bangarori da dama.

Ya bayyana cewar ya yi wa shugaba Buhari yakin neman zabe a 2015 amma ya dawo daga rakiyar gwamnatin sa bayan rashin gamsuwa da kokarin ta.

DUBA WANNAN: Sakamako: Buhari ya kayar da Atiku da fifikon kuri’u fiye da 900,000 a Katsina

A yayin da INEC ke cigaba da karbar sakamakon zabe daga baturan zabe na jihohi, shugaba Buhari na cigaba da bawa Atiku ratan kuri'u ma su yawa.

Sai dai har yanzu INEC ba ta kammala karbar sakamakon ba balle ta sanar da wanda ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a tsakanin Atiku da Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel