Chabb! Babbar Magana, sai da Amaechi ya kawo wa Buhari manyan yankunan jihar Ribas duk da kokarin su Wike

Chabb! Babbar Magana, sai da Amaechi ya kawo wa Buhari manyan yankunan jihar Ribas duk da kokarin su Wike

- Sakamakon zaben karamar hukumar Emohua ta jihar Rivers na nuna shugaba Buhari ne ya lashe

- Hakan ya jawo hargitsi da hayaniya daga wakilan jam'iyyar adawa

- Duk da shugaba Buhari kananan hukumomi hudu ya kawo a jihar inda Atiku ya kawo 14

Chabb! Babbar Magana, sai da Amaechi ya kawo wa Buhari manyan yankunan jihar Ribas duk da kokarin su Wike
Chabb! Babbar Magana, sai da Amaechi ya kawo wa Buhari manyan yankunan jihar Ribas duk da kokarin su Wike
Asali: Depositphotos

Sakamakon zaben karamar hukumar Emohua na jihar Rivers ya fito inda shugaba Muhammadu Buhari ya lashe da kuri'u 72,745 kamar yanda alkalin zabe Aniefiok Essien ya samu.

An karbi sakamakon duk da zanga zanga da tashin tashina da wakilan jam'iyyar adawa suka dinga.

Mr Essien ya tabbatar dacewa za a hada da sakamakon a takardar sakamakon zabe ta jihar kafin a mika ta ga hukumar zabe ta kasa.

Da farko dai Mr Essien yace za a dubi sakamakon Emohua a matsayin sakamako na musamman bayan da EO Kenneth Ita da CO Pang Enubari suka kawo sakamakon a karo na uku.

Wakilan jam'iyyar PDP karkashin jagorancin PDP Austin Okpara sun tada hargitsi tare da hayaniya bayan da EO yaki karbar sakamakon tare da bukatar ingantaccen bayani akan yanda CO din ya samo su.

Amma sai aka sanar cewa daga baya an sasanta a karo na biyu inda a karo na uku EO din ya karba.

Wakilan APC biyu da suka shiga dakin karbar sakamakon bayan da karamar hukumar Emohua suka kawo sakamakon sunce wakilan dake tada hargitsi a gurin wakilan PDP ne da ke rataya da shaidar wasu jam'iyyu.

DUBA: An dawo da 'yan Najeriya 166 daga Libya, an kamo masu kai su su bautar su biyu

A sakamakon APC ta samu kuri'u 72,745 sai PDP ta samu 7148.

Bayan karamar hukumar Emohua, Mr Buhari yaci wasu kananan hukumomi a jihar da suka hada da Opobo/Nkoro, Asari Toru da Obua Odua ta jihar Rivers.

Mr Abubakar ya lashe kananan hukumomi 14 da suka hada da Oyigbo, Omuma, Onelga, Eleme, Gokana, Etche da sauran su.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel