Kai tsaye: Hasashen masana ya hango Shugaba Buhari ya kada Atiku Abubakar

Kai tsaye: Hasashen masana ya hango Shugaba Buhari ya kada Atiku Abubakar

Yayin da ake cigaba da gabatar da sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata ga shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC, an yi hasashen lashe zaben shugaba Muhammadu Buhari.

Kamar dai yadda muka samu, tun a jiya Litinin ne aka soma bayyana sakamakon inda kuma a jiyan shugaban kasar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC yake kan gaba da kusan kaso 67 cikin dari na kuri'un da aka bayyana sakamakon su.

Kai tsaye: Hasashen masana ya hango Shugaba Buhari ya kada Atiku Abubakar
Kai tsaye: Hasashen masana ya hango Shugaba Buhari ya kada Atiku Abubakar
Asali: UGC

Shi kuwa dan takarar shugabancin kasar a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a jiyan yana da kaso 33 ne a cikin dari na kuri'un da aka kada daga jahohin da suka bayyana nasu sakamakon.

Haka zalika kamar yadda muka samu, kawo yanzu shugaba Buhari yana da kuri'u sama da miliyan 11 yayin da shi kuma Atiku ABubakar yake da kasa da miliyan 10.

Babban abun lura dai a nan shine yadda shugaba Buhari ya lashe kuri'un jahohin Kano da Legas kasantuwar sune jahohin da suka fi ko ina yawan masu kada kuri'a wanda hakan ne ya bashi karfin gwuiwa sosai.

Haka ma dai yanzu haka akwai sauran jahohin da ke da masu kuri'u da yawa kamar Katsina da irin su Ribas da ake dakun zuwan su kuma ana tunanin shugaba Buhari yayi kokari sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel