PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Shugaban kasa da na majalisa a Kano

PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Shugaban kasa da na majalisa a Kano

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kano tayi wasti da sakamakon zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta tattara a jihar.

Shugaban jam’iyyar a jihar kuma jami’in jam’iyyar a cibiyar hada kuri’u, Rabiu Sulaiman Bichi ya nuna rashin amincewa da yadda aka tafiyar da adadin a lokacin hada kuri’un.

Bichi ya fada ma manema labarai a hedkwatar INEC a Kano cewa ba za su aminta da yawan kuri’un da aka samu daga sakamakon zaben ba.

PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Shugaban kasa da na majalisa a Kano
PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Shugaban kasa da na majalisa a Kano
Asali: UGC

Da aka tambaye shi ko PDP za ta dauki wani mataki na doka akan lamarin, Bichi ya bayyana cewa za su yi duba zuwa ga yiwuwar hakan sannan su ga mai doka za ta yi akan hakan domin su bi hakkinsu.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya lashe jihar Niger da kuri’u 612,371

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a yayin da tiryan-tiryan sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar ke ci gaba da bayyana, mun samu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Atiku Abubakar diban Karan Mahaukaciya a jihar Kano.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari da ya kasance dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya yiwa abokin adawar na jam'iyyar PDP, Atiku, bugun dawa yayin da hukumar zabe ta kasa ta kammala kididdiga da kidayar sakamakon zaben jihar Kano.

Shafin jaridar Sahara Reporters ya ruwaito cewa, Shugaban kasa Buhari ya yi nasara cikin dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar Kano yayin da Atiku ya tashin fam-fam-fam ba tare da samun nasara a ko guda ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, Buhari ya kare martabar mahaifar sa ta jihar Katsina inda ya lallasa Atiku da fifikon kuri'u 900,000. Kazalika Atiku ya kare martabar mahaifar sa ta jihar Adamawa, inda ya yiwa Buhari shigar wuri da kimanin kuri'u 410,266.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel