Sakamakon zabe: Atiku ya ragargaji Buhari a jihar Anambra

Sakamakon zabe: Atiku ya ragargaji Buhari a jihar Anambra

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta sanar da sakamakon zabukkan da aka gudanar a kananan hukumomi 21 da ke jihar Anambra inda Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 524,738.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya lashe zabe a dukkan kananan hukumomi 21 da ke jihar Anambra inda shi kuma abokin hammayarsa Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 33,298.

Shugaban jami'ar Michael Okpara da ke Umudike, Farfesa Francis Otunta wanda shine baturen zaben shugaban kasa na jihar ne ya bayyana sakamakon zaben na 2019 a safiyar ranar Lahadi a Awka.

DUBA WANNAN: Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani

Sakamakon zabe: Atiku ya lallasa Buhari a jihar Anambra
Sakamakon zabe: Atiku ya lallasa Buhari a jihar Anambra
Asali: Facebook

Otunta ya ce Mr John Gbor na jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), ya samu kuri'u 30,034 inda ya zama na uku shi kuma Farfesa Kingsley Moghalu na Jam'iyyar Young Progressives Party, YPP ya samu kuri'u 4,091.

Ya ce mutane 2,389,332 ne su kayi rajitsan zabe a jihar kuma a cikinsu 675,273 ne aka tantance a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019 domin kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Ya ce an kada kuri'u 605,734 amma cikinsu 19,301 ba su da kyau.

A cewar Otunta, "Za a mika sakamakon zaben da aka tattara zuwa ga hedkwatan INEC da ke Abuja inda za a hada da sakamakon zabukkan sauran jihohin Najeriya har da babban birnin tarayya Abuja kafin a sanar da wanda ya lashe zaben."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel