Abdulaziz Yari ya lashe kujerar sanata a yankin Zamfara ta yamma

Abdulaziz Yari ya lashe kujerar sanata a yankin Zamfara ta yamma

- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Gwamna Abdula’ziz Yari na jihar Zamfara a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata a yankin Zamfara ta yamma

- Yankin na dauke da Kananan hukumomin shida da suka hada da Anka, Bakura, Bukkuyum, Gummi, Maradun da kuma Talata-Mafara

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Gwamna Abdula’ziz Yari na jihar Zamfara a matsayin wanda ya lashe zaben Sanata a yankin Zamfara ta yamma a zaben da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa yankin na dauke da kananan hukumomi shida.

Abdulaziz Yari ya lashe kujerar sanata a yankin Zamfara ta yamma
Abdulaziz Yari ya lashe kujerar sanata a yankin Zamfara ta yamma
Asali: UGC

Kananan hukumomin sun hada da Anka, Bakura, Bukkuyum, Gummi, Maradun da kuma Talata-Mafara.

Da yake sanar da sakamakon zaben a Talata-Mafara a ranar Litinin, Jami’in zabe, Farfesa Lawal Mayanchi, yace Yari na APC na da kuri’u 153, 626 yayinda Lawal Hassan na PDP ked a kuri’u 69,293.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya lashe jihar Niger da kuri’u 612,371

Wani jigon APC a jihar, Alhaji Sha’ayau Sarkin-Fawa, ya bayyana nasarar a matsayin ci gaba mai kyau.

Sarkin-Fawa yace Yari ya cancanci wakiltan jihar a majalisar dattawa, duba ga irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a shekaru takwas da suka gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel