Buhari ya lashe jihar Niger da kuri’u 612,371

Buhari ya lashe jihar Niger da kuri’u 612,371

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kuri’u 612,371 a jihar Niger

- Babban abokin adawarsa Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri’u 218,052

- Buhari ne ya lashe zaben shugaban kasa a jihar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben ranar Asabar da ya gabata, ya samu kuri’u 612,371 a jihar Niger.

Farfesa Anjela Mary, jami’ar hada zaben shugaban kasa a jihar, ya sanar da hakan a hedkwatar INEC a Minna a ranar Litinin.

Buhari ya lashe jihar Niger da kuri’u 612,371
Buhari ya lashe jihar Niger da kuri’u 612,371
Asali: UGC

Mary, wacce ta kasance shugabar jami’ar Lokoja tace Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya samu kuri’u 218,052.

Ta bayyana cewa adadin wadanda aka yiwa rijista sun kasance 2,375,568 yayinda aka tantance 911,964.

Mary ta kara da cewa adadin kuri’u masu amfani ya kasance 851,937 yayinda aka yi watsi da 45,039.

KU KARANTA KUMA: Sakamakon zabe: Hadimin El-Rufai ya yi ma Shehu Sani rubdugu a zaben Sanata

Ta kuma bayyana cewa kuri’un da aka kada sun kasance 896,976.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel