Zaben 2019: Atiku ya lallasa Buhari a jihar Edo

Zaben 2019: Atiku ya lallasa Buhari a jihar Edo

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lallasa shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a jihar Edo da ke Kudancin kasar nan.

Yayin da tiryan-tiryan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ke bayyana sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, mun samu cewa tsohon mataimakin shugaban kasa ya yiwa Buhari mugunyar kaye a jihar Edo.

Kamar yadda Ndowa Lare, alkalin zabe reshen jihar Edo ya bayyana, Wazirin Adamawa ya samu gamayyar kuri'u 275,691 da ta sanya ya lallasa Buhari mai kuri'u 267,691 bayan kammala kididdiga da kidaya a birnin jihar na Benin.

Zaben 2019: Atiku ya lallasa Buhari a jihar Edo
Zaben 2019: Atiku ya lallasa Buhari a jihar Edo
Asali: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku mai rinjayen nasara a kananan hukumomi takwas na jihar Edo, shugaban kasa Buhari cikin rashin sa'a ya samu nasara a kananan hukumomi goma na jihar.

KARANTA KUMA: Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da Borno

Atiku wanda ya lashe zaben a jihar Edo ya samu nasara a kananan hukumomi da suka hadar da; Esan North East, Ovia North East, Egor, Oredo, Esan South East, Esan West, Esan Central da kuma Ipoba-Okha.

Shugaban kasa Buhari ya yi nasara a kananan hukumomi da suka hadar da; Etsako West, Akoko-Edo, Igueben, Ovia South West, Etsako East, Owan East, Owan West and Esako Central, Uhumwonde da kuma Orhionwon.

Tiryan-Tiryan ga yadda ta kaya tsakanin shugaban kasa Buhari da Atiku a kananan hukumomin jihar Edo

Etsako Central LGA

APC: 11,437

PDP: 9,011

Owan West LGA

APC: 12,524

PDP: 10,758

Esan North East LGA

APC: 7,991

PDP: 13,361

Owan East LGA

APC: 18,678

PDP: 15,221

Etsako East LGA

APC: 16,151

PDP: 16,146

Ovia North LGA

APC: 12,612

PDP: 15,706

Ovia South LGA

APC: 11,511

PDP: 9,987

Egor LGA

APC: 12,482

PDP: 23,566

Oredo LGA

APC: 21, 496

PDP: 34, 841

Esan South LGA

APC: 11,039

PDP: 11,435

Esan West LGA

APC: 10,596

PDP: 16,013

Igueben LGA

APC: 7,503

PDP: 6,553

Akoko-Edo LGA

APC: 23,945

PDP: 17,511

Ipoba-Okha LGA

APC 25,404

PDP 30,122

Etsako West LGA

APC: 31,336

PDP: 11,395

Esan Central LGA

APC: 8,691

PDP: 9,512

Uhumwonde LGA

APC: 9,969

PDP: 9,766

Orhionwon LGA

APC: 15,099

PDP: 13,787

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel