Ifeanyi Ubah ya doke Chris Ubah da Andy Ubah a zaben Majalisar Dattawa

Ifeanyi Ubah ya doke Chris Ubah da Andy Ubah a zaben Majalisar Dattawa

Mun ji labari cewa jam’iyyar nan ta YPP watau Young Progressive Party tayi nasara wajen lashe kujerar ‘dan majalisar dattawa a cikin jihar Anambra. YPP ta doke PDP da APGA da kuma ma jam’iyyar APC.

Ifeanyi Ubah ya doke Chris Ubah da Andy Ubah a zaben Majalisar Dattawa
Ubah ya doke ‘Yan gidan Ubah a kujerar Sanatan Yankin Anambra
Asali: Depositphotos

Shugaban kamfanin nan na Capital Oil and Gas, masu harkar man fetur watau Ifeanyi Ubah, ya lashe zaben majalisar dattawa na kudancin jihar Anambra da aka yi a karkashin jam’iyyar YPP wanda ba ta da farin jini sosai.

‘Dan takarar ya samu kuri’a 87, 081 ne inda ya doke ‘dan takarar PDP watau Chris Uba wanda ya samu kuri’a 62, 462. Sanata Andy Uba wanda yake kan kujerar a yanzu ya zo na uku ne a zaben bayan ya samu kuri’u har 13, 245.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya hango shan kayi a zaben 2019 yayi ragas

‘Dan takarar jam’iyyar nan ta APGA watau Nicholas Ukachukwu, shi ne ya zo na uku a zaben, Nicholas Ukachukwu ya samu kuri’u 51,269 ne a zaben kamar yadda malamin zaben yankin mai suna M.N Umenweke ya bayyana.

Hukumar INEC ta sanar da Patrick Ifeanyi Ubah a matsayin wanda ya ci kujerar Sanatan yankin bayan ya zarcewa sauran ‘yan takara 26 a yawan kuri’u. Ifeanyi Ubah ya takawa ‘Yan gidan Ubah burkin zama Sanata a wannan karo.

Tun 1999 dai Mutanen gidan Ubah ne su ke yin Sanata a yankin na Kudancin Anambra. A 1999, Babban Namjin gidan, Dr Ugochukwu Uba, ne ya wakilci yankin. Yanzu kuma Andy Ubah yake kai, inda Chris Uba ya zo na 2 a zaben bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel