Yadda Buhari ya yi biji biji da Atiku Abubakar a sakamakon zaben jahar Kebbi

Yadda Buhari ya yi biji biji da Atiku Abubakar a sakamakon zaben jahar Kebbi

Tun bayan kammala kada kuri’u a zaben shugaban kasa daya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Feburairu ne aka shiga kidaya tare da tattara alkalumman sakamakon zaben daga kowace rumfa, kowacce mazaba, karamar hukuma, jaha da ma kasa baki daya.

Sai dai zuwa yanzu mutane biyu kacal ake jin amonsu daga cikin yan takarar shugaban kasa saba’in da daya, sune yan takarar jam’iyyar APC, Muhammadu Buhari da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige Dansanda yayin rakiyar sakamakon zabe

Kuma zuwa yanzu duka yan takaran biyu suna doke ni, in dokeka, amma fa irin na kuri’u, a jihohi daban daban, sai dai a jahar Kebbi, Buharin ne ya doke Atiku, kai a iya cewa ma Buhari ya lallasa Atiku lilis duba da alkalumman sakamakon zaben da aka bayyana na kananan hukumomi 19 cikin 21 dake jahar.

Legit.ng ta kawo muku sahihai, ingantattu kuma tabbatattun sakamakon zaben da turawan zaben shugaban kasa suka sanar a jahar Kebbi na kananan hukumomi 19 kamar haka, yayin da ake sauraron kananan hukumomin Gwandu da Augie:

Fakai

APC: 12, 200

PDP: 4,865

Danko-wasagu

APC: 31,818

PDP: 8,724

Yauri

APC: 24,677

PDP: 7,108

Zuru

APC: 23,520

PDP: 12,326

Dandi

APC: 26,512

PDP: 7,442

Bunza

APC: 20,622

PDP: 6,285

Aliero

APC-17,863

PDP-5,458

Kalgo

APC-19,058

PDP-3,233

Ngaski

APC-20,641

PDP-3591

Sakaba

APC-14,026

PDP-3,800

Suru

APC-22,627

PDP-10,358

Shanga

APC-19,262

PDP-6,961

Bagudo

APC-29,243

PDP-8,160

Arewa

APC-32,582

PDP-8,390

Jega

APC : 42,970

PDP: 7,416

Birnin Kebbi

APC: 71,510

PDP: 12,900

Koko/Besse

APC: 25,874

PDP: 5,668

Maiyama

APC: 3001

PDP: 6, 279

Argungu

APC: 42038

PDP: 6,951

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel