Sakamako: Buhari ya kayar da Atiku da fifikon kuri’u fiye da 900,000 a Katsina

Sakamako: Buhari ya kayar da Atiku da fifikon kuri’u fiye da 900,000 a Katsina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mai neman tazarce a karkashin jam’iyyar APC, ya lashe zaben kujerar shugaban kasa a Katsina, jihar sa ta haihuwa.

A sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar a fadin kasar nan, shugaba Buhari ya samu nasara a kananan hukumomin jihar Katsina 34 kamar yadda baturiyar hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Fatima Mukhtar, ta sanar.

Farfesa Fatima ta sanar da cewar Buhari ya samu kuri’u 1,232,133 da su ka bashi nasara a kan abokin takarar sa, Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 308,056.

Sakamako: Buhari ya kayar da Atiku da fifikon kuri’u fiye da 900,000 a Katsina
Buhari a Katsina
Asali: Facebook

An samu banbancin kuri’u 924,077 a tsakanin Buhari da Atiku.

DUBA WANNAN: Atiku ya samu nasara a kan Buhari da kuri’u 548,665 a jihar Filato

Ana sa ran Farfesa Fatima za ta wuce zuwa Abuja a daren ranar Litinin domin gabatar da sakamakon zaben a gaban shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa ta kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel