Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani

Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta ce babu wani hujja ko dalili da zai sanya jam'iyyar PDP ta ce ba za ta amince da sakamakon zaben shugaban kasa da na dan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata ba.

A halin yanzu dai ana cigaba gabatar da kuri'un da aka kidaga ga shugaban INEC a dakin taron sanar da sakamakon zabe na International Conference Centre (ICC), da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Sakataren yada labarai na INEC, Mr Rotimi Oyekanmi ya shaidawa Daily Trust cewa hukumar tana gudanar da ayyukan ta kamar yadda ya dace kuma ba ta son yin rikici da kowane jam'iyya.

DUBA WANNAN: Shekarau zai canji Kwankwaso a majalisar dattijai

Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani
Kin amincewa da sakamakon zabe: INEC ta mayarwa PDP martani
Asali: UGC

"Sakamakon zaben da aka sanarwa ba bu kuskure a ciki. An tantance dukkan sakamakon. Ba mu kammala sanar da sakamakon zabukkan ba. Sakamakon Jihohi 10 muka kammala saboda haka akwai sauran jihohi da ke tafe.

"Saboda haka zamu cigaba da gudanar da aikin mu cikin kamar yadda kowa ke sa ran zamu yi. Abinda muke aikatawa shine ya dace," inji Oyekanmi.

A baya dai jam'iyyar PDP ta nemi a soke sakamakon zabukkan inda tayi ikirarin cewa an tafka magudi a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel