Atiku ya samu nasara a kan Buhari da kuri’u 548,665 a jihar Filato

Atiku ya samu nasara a kan Buhari da kuri’u 548,665 a jihar Filato

Atiku Abubakar, dan takarar neman zama shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya lashe zabe a jihar Filato da kuri’u 548,665.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku, ya samu nasara a kan abokin hamayyar sa, Muhammadu Buhari, dan takarar jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 468,555.

Farfesa Richard Kimbir, baturen tattara sakamakon zabe a jihar Filato, ne ya sanar da sakamakon zaben ranar Litinin a garin Jos.

Farfesa Kambir, shugaban jami’ar koyar da harkokin noma ta tarayya da ke jihar Benuwe, ya ce Atiku ya samu nasara a kananan hukumomin 11, yayin da Buhari ya samu nasara a kananan hukumomi 6.

Ga sakamakon zaben kamar yadda Farfesa Kambir ya sanar:

Kanam

APC: 51, 017

PDP: 18, 331

Wase

APC : 35, 931

PDP : 22, 809

Jos Ta Arewa

APC :93, 800

PDP : 53, 277

Mangu

APC : 42, 947

PDP: 48, 923

Shendam

APC : 38, 196

PDP :24, 162

Barkin Ladi

APC : 15, 390

PDP : 42, 138

Bassa

APC : 27, 632

PDP : 34, 822

Langtang Ta Arewa

APC: 16, 665

PDP: 34, 105

Riyom

APC : 8, 710

PDP : 21, 892

Bokkos

APC 18, 328

PDP : 32, 246

Jos Ta Kudu

APC : 25, 574

PDP: 106, 526

Qua’anpan

APC : 20, 872

PDP : 17, 479

Lantang Ta Kudu

APC 11, 224

PDP : 18, 470

Pankshin

APC : 21, 609

PDP: 30, 509

Kanke

APC 17, 946

PDP : 22, 875

Mikang

APC: 10, 869

PDP : 11, 262

Jos Ta Gabas

APC : 11, 847

PDP: 8, 853. (NAN)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel