APC ta kalubalanci nasarar da Atiku ya samu a kananan hukumomi 3 a Adamawa

APC ta kalubalanci nasarar da Atiku ya samu a kananan hukumomi 3 a Adamawa

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a zaben jihar Adamawa inda ya samu kuri'u 410,266 yayin da Buhari ya samu 378,072.

Sai dai bayan an kammala bayyana sakamakon zaben na kananan hukumomi, wakilin jam'iyyar APC ya ki amincewa da nasarar da Atiku ya yi wasu kananan hukumomi uku sune - Numan, Michika da Madagali inda ya ce rikicin makiyaya ya mamaye Numan yayin da Boko Haram sun tarwatsa al'umma a Michika da Madagali saboda haka zai yi wahala al'ummar kananan hukumomin su sami katin zabe.

Ya yi ikirarin an kirkiri sakamakon zaben ne sai dai sauran wakilan jam'iyyun da suka fafata a zaben ba su bashi goyon baya ba.

APC ta kalubalanci nasarar da Atiku ya samu a kananan hukumomi 3 a Adamawa
APC ta kalubalanci nasarar da Atiku ya samu a kananan hukumomi 3 a Adamawa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: Atiku ya doke Buhari a jihar Oyo

Tuni dai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta amince da sakamakon inda ya bayyana Atiku a matsayin wanda ya lashe zabe a jihar.

Ga sakamakon zabukan kananan hukumomin a kasa:

Hong LGA

APC 20,471

PDP 23,039

Ganye LGA

APC 20,360

PDP 17,770

Guyuk LGA

APC 10,825

PDP 22,059

Lamurde LGA

APC 8,123

PDP 21,404

Yola South LGA

APC 34,534

PDP 20,414

Mubi South LGA

APC 19,361

PDP 10,514

Mubi North LGA

APC 26,746

PDP 23,156

SHELLENG LGA

APC 13,531

PDP 11,912

Girei LGA

APC 17,765

PDP 14,673

Yola North LGA

APC 43,865

PDP 27,789

Numan LGA

APC 10,610

PDP 23,469

Demsa LGA

APC 6,989

PDP 29,997

Mayo- Belwa LGA

APC 20,842

PDP 23,734

Madagali LGA

APC 8,208

PDP 14,594

Maiha LGA

APC 17,034

PDP 7,916

Song LGA

APC 17,350

PDP 22,648

Fufore LGA

APC 29,507

PDP 16,430

Gombi LGA

APC 12,805

PDP 18172

Jada LGA

APC 21,332

PDP 22,877

Michika LGA

APC 10,669

PDP 32,085

Toungo LGA

APC 7,145

PDP 5,614

Asali: Legit.ng

Online view pixel