Da dumin sa: Sanata Akpabio na APC ya sha mummunan kaye hannun PDP a Akwa Ibom

Da dumin sa: Sanata Akpabio na APC ya sha mummunan kaye hannun PDP a Akwa Ibom

Sakamakon zabe dai na cigaba da bayyana a hukumance daga bakin hukumar zabe mai zaman kan ta ta Kasa watau INEC inda wasu sakamakonnin ke cike da ban mamaki da al'ajabi wasu kuma suke ke zuwa kamar yadda aka zata daman.

Yanzu wani rahoto da muka samu ya nuna cewa Sanata Godswill Akpabio na jam'iyyar mai mulki ta APC daga jihar Akwa Ibom ya sha mummunan kaye a hannun abokin hamayyar sa daga jam'iyyar PDP a zaben da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata.

Da dumin sa: Sanata Akpabio na APC ya sha mummunan kaye hannun PDP a Akwa Ibom
Da dumin sa: Sanata Akpabio na APC ya sha mummunan kaye hannun PDP a Akwa Ibom
Asali: Facebook

Mun samu cewa Sanata Akpabio, dake zaman tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar ta dattawa na APC ya samu kuri'u 67, 487 kacal yayin da kuma Mista Chris Ekpenyong daga PDP ya samu kuri'u 136, 373.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel