Jam’iyyar PDP ta nemi a saki Buba Galadima da aka garkame

Jam’iyyar PDP ta nemi a saki Buba Galadima da aka garkame

Mun ji labari cewa babbar jam’iyyar adawar Najeriya watau PDP tayi kira ga jami’an tsaron Najeriya su gaggauta sakin Buba Galadima wanda yake tsare a hannun hukuma tun jiya Ranar Lahadi.

Jam’iyyar PDP ta nemi a saki Buba Galadima da aka garkame
An yi awon gaba da Jagoran adawa Buba Galadima a Najeriya
Asali: UGC

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa baki daya, Prince Uche Secondus, shi ne ya fitar da jawabi yana mai kira ga hukumar DSS masu fararen kaya ta fito da Injiniya Buba Galadima da aka damke jiya bayan ya fito yayi wasu maganganu.

Jam’iyyar adawar ta nemi ayi maza a saki Buba Galadima tun da girma da arziki inda ya zargi jami’an DSS da hada kai da jam’iyyar APC mai mulki wajen kassara ‘yan adawa. Yanzu dai babu wanda ya san inda Buba Galadima yake.

KU KARANTA: Buhari yana cigaba da aman kuri'u a cikin Jihar Kano

PDP tace bai dace a kama mutum irin Buba Galadima wanda aka sani da kishin kasa da kare hakkin Bil Adama da asassa tafiyar damukaradiyya a Najeriya. Secondus yace ko shugaba Buhari ya sa irin kokarin da Galadima yayi a baya.

Shugaban jam’iyyar adawa ya koka da yadda aka yi ram da Kakakin yakin na neman zaben ‘dan takarar Atiku Abubakar watau Alhaji Buba Galadima bayan kwamitin yakin neman zaben Buhari tayi kira ga jami’an tsaro su damke shi.

Galadima dai ya fito bayan zabe yana kira ga jama’a cewa su tsaya tsayin-daka domin hana jam’iyyar APC murde zaben da aka yi. Tun bayan wannan magana ne dai wasu su ka yi gaba da shi har yau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel