Yanzu-yanzu: Bamu yarda da sakamakon zabe ba - Shugaban PDP

Yanzu-yanzu: Bamu yarda da sakamakon zabe ba - Shugaban PDP

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ba ta amince da sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ke fitarwa ba a halin yanzu.

Shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus wanda a halin yanzu ya kira taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja ya ce kuri'un da INEC ke sanarwa ba dai-dai bane kuma ba za su amince da hakan ba.

Yanzu-yanzu: Bamu yarda da sakamakon zabe ba - Shugaban PDP
Yanzu-yanzu: Bamu yarda da sakamakon zabe ba - Shugaban PDP
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sakamakon zabe: Atiku ya doke Buhari a jihar Oyo

A wata labarin, Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya na jam'iyyar PRP ya nemi hukumar INEC ta soke zaben 'yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar Kaduna.

Shehu Sani ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a garuruwa da yawa da ke karkashin mazabarsa kuma ya ce idan har INEC na son yin adalci ya zama dole ta soke zaben.

Ku biyo mu domin samun karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel