Shehu Sani ya nemi a soke zaben majalisar tarayya a Kaduna

Shehu Sani ya nemi a soke zaben majalisar tarayya a Kaduna

Dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bukaci a soke zaben majalisar tarayya da ake gudanar a jihar Kaduna.

Sanatan ya yi wannan kiran ne a taron manema labarai a Kaduna inda ya ce an tafka magudi a zaben da akayi.

Ya ce ba ayi zabe ba a mafi yawancin kananan hukumomi da ke karkashin mazabarsa kamar Giwa, Birnin Gwari da Igabi.

Shehu Sani ya yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta soke zaben muddin tana son yin adalci.

DUBA WANNAN: Zabe: Sakamako daga jihohin Sokoto, Kebbi da Jigawa

Shehu Sani ya nemi a soke zaben majalisar tarayya a Kaduna
Shehu Sani ya nemi a soke zaben majalisar tarayya a Kaduna
Asali: UGC

"Mun damu a kan rahotannin sayan kuri'u, magudin zabe da matsalolin na'urar tantance katin zabe da wakilan mu suka bayyana mana. An kuma samu wuraren da adadin mutanen da suka kada kuri'a sun dara jimilan mutanen da sunayen su ke rajistan zabe.

"Hakan ya faru ne saboda ba a tantance masu zabe. A karamar hukumar Giwa, ma'aikatan wucin gadi da suka gudanar da zabe ba su samu horo daga INEC ba. A Birnin Gwari, an tafka magudi tare da musgunawa masu zabe," inji shi.

Shehu Sani ya kuma ce ba a samar wa al'umma Igabi takardun kada kuri'a a kan lokaci ba.

Ya ce jam'iyyarsa ta PRP ta shigar da korafi ga Hukumar INEC inda ta ke bukatar a soke dukkan zabukan da aka gudanar a jihar musamman na Sanata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel